Ya Zama Dole PDP Ta Bar Shugabancin Kasa A Arewa – Mr LA

Honorabul Lawal Adamu Usman, ya bayyana cewa ya zama wajibi PDP ta kai tikitin takarar shugaban ƙasan ta yankin arewa saboda dabarun yaƙi irin na siyasa.

Mista LA’ ya yi wannan furuci ne a Zariya, yayin da yake zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ranar Lahadi.

“Saboda dabaru da kuma amfanin jam’iyya da ƙasa baki ɗaya, ya zama wajibi PDP takai tikitin shugaban ƙasa Arewa a babban zaɓen 2023.”
Mista LA ya bayyana cewa dalilan da yasa ya zama wajibi akan PDP ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga Arewa shine saboda adalci da dai-daito.

“Saboda adalci da kuma baiwa kowane yanki haƙƙinsa, Arewa ya dace ta fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 ƙarƙashin Jam’iyyar PDP.”

“PDP ta shafe shekaru 16 a kan madafun iko, yankin kudu maso gabas sun yi jagoranci na shekara 8 ƙarƙashin Obasanjo, kudu maso gudu sun kwashe shekaru 6 karkashin Jonathan.”

“Amma baki ɗaya yankin arewa, arewa ta tsakiya, arewa ta gabas da arewa ta yamma sun yi jagoranci na shekara biyu ne kacal karkashin marigayi Yar’adua.”

Mista LA’ wanda tsohon ɗan takarar kujerar sanatan Kaduna ta tsakiya ne, yace PDP ta fi yawan magoya baya a yankin arewa fiye da sauran sassan ƙasar nan.

“Adadin magoya bayan PDP da ake da su a baki ɗaya sassan arewa kaɗai sun isa a duba a baiwa yankin tikitin takarar shugaban ƙasa.”
“Idan muna son PDP ta farfaɗo to wajibi mu lashe zaben 2023, kuma idan muna son cimma haka sai an kai tikiti arewa.”

“Ina da yakinin cewa zamu samu nasara a zaɓen dake tafe matukar aka tsayar da ɗan arewa takarar shugaban ƙasa.”

Labarai Makamanta