Ya Zama Dole Almajirai Su Bar Kaduna – El Rufa’i

Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta lamunci ganin makarantun Almajirci a jihar ba, ya yi kira da su tattara inasu-inasu su bar jihar.

Malam El-Rufa’i ya bayyana hakan ne yayinda rantsar da kwamitin kare hakkin yara da jin dadinsu a ranar Talata, 9 ga Maris, 2021.

Yace: “Muna aiki kan lamarin Almajiranci kuma mutane da dama basu yarda da abin da muke yi ba, amma muna da tabbacin cewa hakan ne abin da ya dace muyi.”

“Saboda haka, sako na ga dukkan masu Almajirai a jihar Kaduna shine su na da damar komawa wata jihar, idan ba haka ba zamu damke mutum.”

“Muna son talakawa su amfana. Yan siyaaa na shiga lamarin da sa ran za a basu wani adadin mutanen da zasu kawo kuma idan aka basu ba maras galihu zasu baiwa ba,”

“Muna son talakawa su amfana. Yan siyasa na shiga lamarin da sa ran za a basu wani adadin mutanen da zasu kawo kuma idan aka basu ba maras galihu zasu baiwa ba,” yace.

“Saboda hakan wajibi ne mu samar da hanyar gane talakawa da marasa hali domin basu irin wannan tallafi.”

Gwamnan ya ce ofishin jin dadin al’ummar jihar na gudanar da ayyuka a kananan hukumomin jihar 23 domin samar da wani takarda na talakawana dake jihar.

A cewarsa, kawo yanzu an samu rijistan gidaje milyan guda kuma ya bada tabbacin cewa tallafin gwamnati zai isa ga wadanda sunayensu ke cikin takardar.

Labarai Makamanta