Ya Zama Dole A Kara Kuɗin Litar Mai A Najeriya – NNPC

Gwamnatin Buhari ta bayyana cewa ko bajima ko badade sai an sayi lita daya ta man fetur naira 234, domin ana sayarwa ne naira 162 a yanzu, saboda gwamnati na biyan naira bilyan 120 kudin tallafin fetur, wato ‘subsidy’ a duk wata.

Shugaban NNPC Mele Kyari ne ya bayyana haka a wani taron musamman na kwamitin da shugaban kasa ya kafa.

Ya ce a duk lokacin da aka sayar da litar fetur naira 162, to NNPC ke cika sauran gibin kudaden, wanda dimbin asara ce kawai gwamnati ke dibgawa.

Kyari ya ce gaskiyar magana, litar man fetur daya ta na kamawa naira 234 idan aka hada kudaden da aka sayo ta a waje, da kudin dako da kuma kudin saukale.

“Saboda haka nan gaba kadan, ko kuma can gaba, ko an ki ko an so sai ’yan Najeriya sun sayi litar fetur naira 234.”

Ko a jawabin da ya yi a wurin, Kyari bai fito karara ya ce kudin ‘subsidy’ gwamnatin Buhari ke biya duk wata har naira bilyan 120 ba.

Cewa ya yi “ana biyan naira biliyan 120 domin a cike gibin adadin kudin da ya kamata a sayar da litar fetur, wato naira 234, ba naira 162 ba.”

Wannan adadi da ya bayyana kuwa ya zo daidai da adadin da PREMIUM TIMES ta yin kirdadon gwamnatin Buhari na biya a duk wata a matsayin tallafin rage kudin farashin litar man fetur, a wani rahoto da ta buga a makon da ya gabata.

Gwamnatin Najeriya na biyan naira bilyan 120 wajen tallafin rage tsadar fetur a duk wata, amma kuma a kasafin 2021, ta ware naira biliyan 70 kadai wajen bunkasa Harkokin Ilmi a Matakin Farko, wato UBEC.

Har ila yau, a makon jiya ne gwamnatin Buhari ta sha ragargaza, biyo bayan fitar da sabon farashin fetur na naira 212 duk lita daya, daga naira 162.

Daga baya gwamnatin tarayya ta dakatar da karin tare da bayyana cewa Hukumar Kayyade Farashin Fetur ce ta yi azarbabin yanka farashin ba tare da sanar da gwamnatin tarayya ba.

Labarai Makamanta