Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta Farfesa Mahmoud Yakubu ya yi kira ga jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a kasar, da su yi duk abin da za su yi domin ganin an daina kai wa kayayyakin zaben 2023 hari a ko ina.
Ya yi wannan kira ne lokacin da yake tattaunawa da majalisar wakilai da kuma kwamiin da yake bincike kan hare-haren da ake kaiwa kan kayayyakin hukumar.
Ya ce hukumar ta fuskanci hare-hare 50 cikin jihohi 15 a 2019, Farfesa Yakubu ya bayyana wasu daga cikin jihohin da abun ya faru da suka hada da Imo wadda aka kai hari 11, sai Osun da ke da bakwai, an kai hare-hare biyar a jihar Enugu.
Sauran sun hada da Akwa Ibom da ita ma akai kai hari biyar, an kai hare-hare hudu a jihohin Cross River da Abiya.
Ya ci gaba da bayyana yadda aka kai hare-hare biyu a jihohin Anambra da Taraba, sai johohin Bayelsa, Ondo, Lagos, Borno, Kaduna da kuma Ogun da dukkansu aka kai musu hari sau daya.
You must log in to post a comment.