Ya Kamata A Zurfafa Bincike Kan Faɗuwar Jirgin Shugaban Dakarun Soji – Ƙungiyar Arewa

An yi kira ga gwamnatin tarayya ƙarkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gudanar da cikakken bincike domin gano makasudin faruwar hatsarin jirgin saman dakarun soji wanda ya yi sanadin mutuwar Shugaban Dakarun Soji da wasu Sojoji a Kaduna.

Kiran ya fito ne daga bakin ɗaya daga cikin Shugabannin Ƙungiyar cigaban yankin Arewacin Najeriya Alhaji Gambo Ibrahim Gujungu, a yayin wata tattaunawa da yayi da manema labarai a Kaduna.

Gujungu ya ƙara da cewar kiran ya zamo wajibi ta la’akari da yadda ake ta samun jita jita da kananan maganganu akan faruwar hatsarin waɗanda ke sanya damuwa, to wannan ba abu bane da za’a yi shiru akai ya zama wajibi ga gwamnati ta gudanar da cikakken bincike domin gano hakikanin abin dake faruwa.

“A fili yake marigayi Janar Attahiru ya ɗauko hanyar gyara ta fuskar inganta tsaro a ƙasar nan, sannan a lokaci guda mutuwa ta ɗauke shi tare da wasu mataimakan shi akan wannan fanni, dole jama’a su zargi wani abu kuma ya dace a gaggauta gudanar da bincike akai”.

Gujungu ya kuma koka da nuna damuwa dangane da yadda sashin Kudancin Najeriya ke murna da mutuwar shugaban Dakarun Sojin, inda yace wannan abin takaici ne kuma ya nuna a fili cewa kasarmu na fuskantar barazana ta kasancewa dunkulalliya, domin a tsarin aikin soja bai kamata ɓangaranci ya shigo ciki ba, aiki ne na kishi da cigaban ƙasa, yayin da aka wayi gari wasu na murna da mutuwar wani jagora a rundunar soji domin kawai bai fito daga yankin su ba babu shakka ana cikin hatsari.

Labarai Makamanta