Ya Kamata A Kara Wa Buhari Wa’adi – Rarara

Shahararren Mawakin Shugaban Kasa Buhari Dauda Kahutu Rarara, ya bayyana cewa ya kamata a kara bawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari dama ya kara shekara shekaru 4 ko 5 bayan kammala wa’adinshi na wannan zango, domin ya ida kammala Ayyukan da ya fara a Najeriya.

Rarara ya bayyana hakan a matsayin ra’ayinshi a yayin tattaunawarshi da sashin BBC Hausa a safiyar ranar Lahadi.

“Da zan bayyanawa ‘yan Najeriya irin Ayyukan da Buhari ya fara gudanarwa a Najeriya da al-umma da kansu zasu karawa Buhari wa’adin shekarun mulki don su mori Alkhairan mulkinshi, injishi.

Labarai Makamanta