Ya Kamata A Jefa Kananan Hukumomi Cikin Al-Jihunan Gwamnoni – El Rufa’i

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa’i, yace jihohi ne ya kamata su yanke kwatankwacin yawan kananan hukumomin da zasu iya ɗauka, saboda haka ya dace a ba Gwamnoni wuka da nama akan kananan hukumomin Jihohin su.

Gwamnan yace Najeriya ƙasa ce dake ɗauke da gwamnatocin jihohi 36 da kuma gwamnatin tarayya, a cewar gwamnan, a lissafo jerin kananan hukumomin ƙasar nan 774 sannan ace ana son maƙala wa gwamnatin tarayya su kai tsaye, wannan ya saɓa wa tsarin mulkin da muke tafiya a kanshi na jamhuriya.

El-Rufa’i yayi wannan jawabi ne a wurin jin ta bakin al’umma kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar nan a ranar Laraba, wanda ya gudana a gidan Gwamnatin Jihar na tunawa da Janar Hassan Usman Katsina dake Kawo Kaduna.

El-Rufa’i yace “Kamata yayi a bar kowace jiha ta yanke adadin yawan ƙananan hukumomin ta waɗanda zata iya samar wa kuɗaɗe kwatankwacin kuɗin shigarta, hakan zai sa a gudanar da gwamnati mai kyau kuma cikin adalci.”

“Kowace jiha ita ya kamata ta duba ta ga tsarin yadda take son kananan hukumominta su kasance, amma dai abunda ake so shine a sanya tsarin demokaraɗiyya a cikin kowane tsari.” “Kuma a ba kowace jiha lokacin gudanar da zaɓen ƙananan hukumominta amma kar ya wuce tsawon shekaru huɗu a tsakani.”

Labarai Makamanta