Yaƙi Da Talauci: Buhari Ya Amince Da Rabawa Matasa Naira Biliyan 75

Majalisar zartaswa ta kasa ta amince da ware N75bn domin samar da shiri na musamman da zai tallafawa matasan kasar, da nufin bunkasa rayuwarsu.

Ministan matasa da Wasanni, Sunday Dare ya bayyana hakan ga ‘yan jaridun fadar shugaban kasa, bayan fitowa daga taron majalisar zartaswar da aka shafe awanni takwas ana yinsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman majalisar zartaswar. A cewarsa, wadanda ke a cikin shekarun samartaka kuma masu tsarin kasuwanci na gaskiya kuma suke zaune a kusa da inda aka gina bankunan ‘yan kasuwa 125 a fadin kasar, kuma suka cancanta ne kawai zasu ci gajiyar tallafin.

Dare ya bata tabbacin cewa kamar yadda akayi shirin N-Power, haka shima wannan zai kasance komai a na’ura kuma za a takaita akan masu shekaru 18 zuwa 35.

Ya jaddada cewa ba za a duba banbanci addini, yare ko tsarin rayuwa wajen bayar da tallafin ba, duk wanda ya cancanta zai ci gajiyar tallafin.

Labarai Makamanta