Yaƙi Da Ta’addanci: Sojin Najeriya Basu Da Kayan Aiki – Shettima

Tsohon Gwamnan Jihar Barno dake Najeriya Kashim Shettima yace sojojin Najeriya basu da isassun kayan aikin da zasu iya murkushe mayakan Boko haram.

Yayin da yake tsokaci kan matsalar tsaro da talaucin da suka addabi yankin arewacin Najeriya, Shettima yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada isassun kudaden da za’a sayawa sojoji kayan aiki amma wadanda aka dorawa hurumin aikin sun gaza.

Tsohon gwamnan yace abin takaici ne yadda matsalar tsaro ke cigaba da addabar Najeriya a karkashin gwamnatin su ta Jam’iyyar APC ba wadda ta kwashe shekaru 6 a karagar mulki, inda ya rantsa cewar muddin gwamnati na da aniyar magance wannan matsala toh abu mai sauki ne a wurin ta.

Dangane da matsalar ilimi kuwa a yankin arewacin Najeriya, Shettima yace abin takaici yadda shugabannin da attajirai ke kwashe ‘yayan su suna kaiwa Turai domin karatu, yayin da aker watsi da ‘yayan talaka.

Tsohon gwamnan yace muddin ana bukatar yaki da talauci a Najeriya toh dole a baiwa ‘yayan talakawa ilimin da ya dace.

Labarai Makamanta