Watsi Da Karɓa-Karɓa: Ra’ayin Mamman Daura Ne Ba Na Buhari Ba – Fadar Shugaban Kasa

Fadar shugaban ƙasa ta ce kalaman Malam Mamman Daura kan batun tsarin karɓa-karɓa a mulkin Najeriya, ba matsayin shugaban ƙasar ba ne ko na gwamnatinsa.

Ta ce maimakon haka, ra’ayinsa na ƙashin kansa a matsayinsa na dattijon ƙasa don haka kalaman ba sa nuni ta kowacce siga da matsayin Shugaba Muhammadu Buhari.
Sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Malam Garba Shehu ya fitar ta ce sun samu ɗumbin buƙatun neman jin ko me za su ce game da hira ta musammam da Malam Daura ya yi da BBC.

A cikin hirar Mamman Daura ya shawarci jam’iyyar APC mai mulki ta fifita cancanta kan la’akari da ɓangare wajen fitar da mutumin da zai gaji kujerar shugaban ƙasa bayan ƙarewar wa’adin Buhari a 2023.

Kalaman na Mamman Daura ga dukkan alamu sun janyo ka-ce-na-ce cikin harkokin siyasar Najeriya, game da makomar shugabancinta bayan kammala wa’adin mutumin da ya fito daga yankin arewa.

Wasu dai na ganin kalaman na baffan shugaban ƙasar kuma babban makusanci ga gwamnatin Buhari tamkar hannunka mai sanda ne ga hasashen da wasu suka daɗe suna yi cewa ba lallai ne mulki ya koma ɓangaren kudancin Najeriya a shekara ta 2023.

Sai dai fadar gwamnati ta kore wannan tunani. A cewarta muhimmin abu ne tun farko a san cewa mai maganar yana bayyana ra’ayinsa ne wanda bai yi nuni ga matsayin shugaban ƙasar ta kowacce irin siga ba.

Ta ƙara da cewa Mamman Daura ya cancanci zama dattijon ƙasa da ke da nauyi a kansa na riƙe wata fahimta kuma ya bayyana ta kamar yadda tsarin mulki da dokokin ƙasar suka tabbatar masa.

Sanarwar ta ce ruɗani ya shigo ciki ne inda kuma wasu suka fara yi wa kalaman fashin baƙi iri daban-daban sakamakon rashin yi wa furucin Mamman Daura adalci a wajen fassara zuwa Ingilishi don yaɗa wannan hira har ma ga mutanen da ba sa jin Hausa.

Ta ce batutuwan da aka tattauna a hirar sun ta’allaƙa ne kan jigon yadda ƙasar za ta samar da wata hanyar tattaunawar siyasa mafi dacewa don kimantawa da ƙiyastawa da kuma fahimtar abubuwan da za su je su komo a siyasance da nufin biyan muradin akasarin ‘yan Najeriya ba tare da la’akarin daga wanne ɓngare suka fito ba.

Labarai Makamanta