Wasu Daga Cikin Ayyukan Sanata Uba Sani A Matakin Kiwon Lafiya (III)

Daga Ibrahim Ibrahim

LAFIYA a ka ce uwar jiki. Sai da lafiya komai ke samuwa a rayuwa. A wannan ɓangaren Sanata Uba Sani ya yi namijin ƙoƙari domin ganin al’ummar sa sun samu sauƙi wajen neman lafiya mai inganci.

Sanatan ya bi lungu da saƙo domin ganin ya inganta harkar lafiya a mazaɓun sa da kuma daukacin Jihar Kaduna baki daya.

Ga kadan daga cikin wasu cibiyoyin kiwon lafiya da Sanata Uba Sani ya gina, kuma ya samar masu da kayan aiki irin na zamani;

Sanata Uba Sani ya gina da samar da kayan aiki na zamani a cibiyar da ke lura da larurorin mata da ke a babban asibitin ƙaramar hukmar Birnin-Gwari.

Ya gina da sanya kayan aiki na zamani a cibiyar da ke lura da larurorin mata da ke a babban asibitin Giwa.

Uba Sani ya gina da sanya kayan aiki na zamani a cibiyar kula da lafiya matakin farko (PHC) da ke a Kasuwan Magani, a ƙaramar hukumar Kajuru.

Sanata Uba Sani gina da gyara gidajen masu duba marasa lafiya da sanya kayan aiki na zamani a cibiyar kula da lafiya matakin farko (PHC) da ke a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.

Sanata Uba ya gina gidajen kwanan malam kiwon lafiya, da gyara da sanyan kayan aiki a cibiyar kula da lafiya matakin farko (PHC) da ke a ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa.

Haka kuma ya gina gidajen kwanan malaman kiwon lafiya, gyara da sanya kayan aiki a cibiyar kula da lafiya matakin farko (PHC) da ke a mazabar Igabi da ke a ƙaramar hukumar Igabi.

Uba Sani ya gyara da gina gidajen kwana na malaman kiwon lafiya da sanya kayan aiki a cibiyar kula da kiwon lafiya matakin farko (PHC) da ke a Unguwan Gaga a mazabar Yakawada da ke a ƙaramar hukumar Giwa.

Ya gina gidajen kwana na malaman kiwon lafiya kashi na 2, gyara da samar da motar ɗaukar marasa lafiya a wurare kamar haka:

Matakin kiwon lafiya na farko da ke a mazabar unguwa a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu.

Matakin kiwon lafiya na farko da ke Afaka a ƙaramar hukumar Igabi.

Matakin kiwon lafiya na farko da ke Maraban Rido a ƙaramar hukumar Chikun.

Matakin kiwon lafiya na farko da ke ƙaramar hukumar Kajuru da sauran su.

Kadan da waɗannan abubuwan a ɓangaren lafiya ƙaɗai aka ɗauka, sun nuna lallai Sanata Uba Sani ya cancanci a zabe shi ya zama Gwamnan Jihar Kaduna.

Zamu Ci Gaba…

Labarai Makamanta