Wasanni: Tottenham Ta Sallami Kocinta

A ranar Litinin mahukuntan kungiyar suka tattauna da Mourinho kafin sallamarsa sakamakon rashin taka rawar gani a gasar cin kofin firamiya ta Ingila.

A wasanninsa biyar na karshe, Mourinho ya samu nasara ne a daya kacal. Bayanai sun nuna cewa Ryan Mason ne zai maye gurbinsa a matsayin kocin riko har zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Mourinho ya maye gurbin Mauricio Pochettino a matsayin kocin Tottenham a watan Nuwamba na 2019.

Tottenham za ta fafata da Manchester City a wasan karshe na gasar cin kofin Carabao ranar Lahadi.

Tottenham na cikin kungiyoyin Premier League shida da suka sanar ranar Lahadi cewa za su kafa sabuwar kungiyar European Super League.

Kazalika kungiyar ta kori masu taimaka wa Mourinho wajen horas da ‘yan wasa wadanda suka hada da Joao Sacramento, Nuno Santos, Carlos Lalin da Giovanni Cerra.

“Jose da masu taimaka masa wajen horas da ‘yan kwallo sun kasance tare da mu a wasu lokuta mafi wahala da kulob din ya tsinci kansa a ciki,” a cewar shugaban Tottenham Daniel Levy. “Jose kwararre ne wanda ya nuna matukar jajircewa lokacin annobar korona.

“A mataki na dangantaka tsakanina da shi na ji dadin aiki tare da shi kuma ina takaicin cewa abubuwa ba su tafi kamar yadda muka yi tsammani ba.

“A kodayaushe za mu yi maraba da shi a nan kuma muna son gode masa da masu taya shi horas da ‘yan wasa bisa kwazonsu.”

Labarai Makamanta