Wasanni: Tottenham Ta Kori Kocinta

Kungiyar Tottenham ta kori Nuno Espirito Santo, bayan wata hudu a kan aikin horar da kungiyar.

A ranar Asabar Manchester United ta je ta doke Tottenham da ci 3-0 a wasan mako na 10 a gasar Premier League.

Tottenham ta sha kashi a wasa biyar daga cikin bakwai da ta fafata a babbar gasar Ingila a bana.

Kungiyar tana ta takwas a teburin Premier da tazarar maki 10 tsakaninta da Chelsea, wadda ke saman teburin kakar bana.

Dan kasar Portugal mai shekara 40 ya karbi aikin horar da Tottenham a watan Yuni, bayan kaka hudu da ya yi a Woolverhampton.

Tottenham ta ce za ta sanar da wanda zai maye gurbin Nuno nan gaba domin jan ragamar kungiyar.

Labarai Makamanta