Wasanni: Ronaldo Zai Tafi Jinya

Ƙungiyar Juventus ta ce dan wasanta na gaba dan kasar Portugal Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan da za ta yi ban a Serie A da kungiyar Atlanta.

Kocin kungiyar Andrea Pirlo ya ce dan wasan mai shekara 36 wanda shi ne ke kan gaba a yawan cin kwallaye da 25, zai huta a wasan gudun kar ya kara samun wani rauni mai hadari.

“Wannan rashin na shi babba ne ga kungiyarmu. Cristiano ba zai buga wasannan na saboda raunin da yake fama da shi,” Pirlo ya shaida wa manema labarai.

“Na kwanaki ya yi ta fama da jinya bayan wasan da muka buga da Genoa.”

Labarai Makamanta