Wasanni: Najeriya Ta Shiga Mataki Na Gaba Bayan Doke Sudan A Gasar Nahiyar Afirka

Kafar tawagar Najeriya daya ta kai zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirca, bayan da ta doke Sudan 3-1 a wasa na biyu a cikin rukuni na hudu ranar Asabar.

Super Eagles ta ci kwallo biyu tun kan hutu ta hannun ‘Samuel Chukwueze da kuma Taiwo Awoniyi.

Bayan da suka koma karawar zagaye na biyu Nageriya ta kara na uku ta hannun Moses Simon.

Sudan ta zare daya a bugun daga kai sai mai tsaron raga ta hannun Walieldin Khidir.

Da wannan sakamakon Super Eagles wadda ta doke Masar da ci 1-0 ranar Talata ta hada maki shida a wasa biyu tana jan ragamar teburi na hudun.

Labarai Makamanta