Wasanni: Morocco Ta Doke Belgium A Gasar Cin Kofin Duniya

Morocco ta bai wa Belgium mamaki bayan ta doke ta 2-0 a wasa na biyu a rukuni na shida a Gasar Kofin Duniya da Qatar ke karbar bakunci.

A minti na 73 Morocco ta ci kwallon farko ta hannun Abdelhamid Sabiri, sannan Zakaria Aboukhlal ya kara na biyu daf da lokaci zai cika.

Mai tsaron ragar Belgium, Thibaut Coutois shi ne ya yi kuren kwallon farko a bugun tazara da Sabiri ya buga masa, saura minti 17 a tashi daga wasan.

A karawar Belgium wadda ba ta taba daukar kofin duniya ba ta je Qatar a matakin ta biyu a kan gaba a taka leda a duniya, biye da Brazil ta farko.

Labarai Makamanta