Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kammala dukkanin shirye shiryen ta na sayen wani yaro mai shekaru 4 mai suna Zayn Ali Salman a matsayin ɗan wasan kungiyar.
Hankalin shugabannin kungiyar ta Arsenal ya kai ga yaron ne a wani wasan ƙwallon ƙafa da yayi, inda suka nemi wakilan da su amince yaron ya ziyarci birnin London.
A tarihin Shahararriyar Ƙungiyar kwallon kafan Zayn Ali Salman ya kasance ɗan wasa mai ƙananan shekaru da ta taɓa saye, kuma sayen nashi ya ɗauki hankalin duniya.
Kocin Kungiyar ta Arsenal Mikel Arteta ya bayyana yaron a matsayin wata ajiyar Allah ta fuskar wasanni wanda zai kafa tarihi a duniyar kwallon kafa.
You must log in to post a comment.