Wasanni: Korar Kocin Newcastle Ta Rikitamu – Kocin Arsenal

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce korar da aka yi wa kocin Newcastle Steve Bruce za ta sanya kociyoyi su rika daina karbar aikin horaswa a kan lokaci.

An kore shi daga kungiyar ne a ranar Laraba, kuma cikin wata tattaunawa da ya yi da Telegraph, Bruce ya bayyana damuwar da ya shiga da shi da iyalansa tsawon shekara biyun da ya yi a kungiyar.

Arteta ya ce da dama daga cikin masu horaswa sun shaida masa cewa dole sai sun yi nazari kafin su karbi aikin horaswar ko wacce kungiya.

“mutane da dama na da irin wannan tunani,” in ji Arteta.

Labarai Makamanta