Wasanni: Gamayyar Kungiyoyin Kwallon Yashi Sun Bude Ofis A Abuja

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

An Bayyana Wasanni a Matsayin Hanyar Taimakawa Matasa da Ayyukan Da Kuma Hanasu Fadawa Ayyukan Ashsha.

Da yake Kaddamar da Ofishin Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa Amaju Pinnick Wanda ya samu Wakilcin Babban Sakataren Hukumar Kwallon Kafa ta Kasa Dr. Muhammad sanusi, Ya Tabbatar da bada Cikakkiyar Gudumawa Ta Kowacce Fuska Don bunkasa Harkokin Wasanni Musamman Kwallon Yashi a Nijeriya, Musamman Ganin yadda Matasa ke Samun aiki Sanadiyyar Wasannin.

Dr. Sanusi ya jinjinawa shugaban Gamayyar Kungiyoyin kwallon Yashi na Africa Mahmud Umar Hadejia tare da masu taimaka masa Don Ganin Wasan Kwallon yashi yaci gaba.

Tunda Farko a nasa Jawabin shugaban Gamayyar Kungiyoyin kwallon Yashi na Africa Mahmud Umar Hadejia yace, Babban manufar wannan aiki shine ciyar da harkar wasan kwallon yashi gaba a nahiyar Afirka. Ya Kara da cewa Bude Wannan sabon Ofishin a Abuja zai taimaka sosai wajen Bunkasa wasan.

Shima a nasa Bayanin Shugaban Kungiyar Kwallon yashi ta Kasa Suleiman Yahaya-Kwande yace kungiyar zata ci gaba da aiki ba dare ba rana Don Ciyar da Harkar Wasan Kwallon Yashi Gaba a Nigeria.

Da Wannan Ci gaba da aka Samu a Bangaren Kwallon yashi na Afirka Ana sa ran Kungiyar Kwallon Kafar yashi ta Nijeriya zata farfado, Bayan Dakatar da Wasanninta da Hukumar Kwallon Najeriya tayi a Baya, Sakamakon Koma baya da ake samu a wasnnin Kwallon Yashin .

Labarai Makamanta