Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sallami mai horar da ‘yan wasanta Ronald Koeman Bayan ya jagoranci kungiyar a wasanni 14 kachal.
A wasan laliga mako na 10 da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta buga a jiya laraba ta sha Kashi da ci daya mai ban haushi daga kungiyar Rayo Vallecano da take Mataki na 5 a teburin laliga.
Ko a ranar lahadi data gabata, kungiyar Barcelona tayi rashin nasara a hannun Realmadrid da ci 2:1 Wanda hakan yasa kungiyar Madrid tai nasara a jere har sau 4 a wasansu da Barcelona a gasar laliga.
Barcelona tayi fama da rashin nasara a wasannin ta inda masana harkar kwallon kafa ke ganin rashin shaharrren Dan wasanta na gaba Messi da ya koma PSG shine dalilin da yasa suke Shan wahala a wasanninta saboda kungiyar Tafi shekaru 10 tana wasa da shaharrren Dan kwallon inda wasu ke ganin kawai rashin shaharrun Yan Wasa ne da mai horar wa.
Yanzu dai Barcelona na Mataki na 9 da maki 15 Bayan buga wasa 10 a kakar bana. Ana dai tsammanin tsohon Dan wasan kungiyar Xavi ne zai maye gurbin Koeman.
A naku fahimtar meya janyowa Barcelona shiga wannan matsalar? Rashin messsi ne ko rashin Mai horaswa?
You must log in to post a comment.