Wasanni: An Nada Sabon Kocin Kungiyar Super Eagles

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta bayar da sanarwar naɗa Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles a ranar Laraba.

Hukumar ta ce Jose Peseiro wanda ɗan asalin ƙasar Portugal ne shi zai maye gurbin Gernat Rohr da ta kora.

Tuni NFF ta naɗa Augustine Eguavoen a matsayin kocin rikon kwarya domin ya ja ragamar Super Eagles a yayin da ake shirin soma gasar cin kofin Afirka.

A cikin sanarwar da ta fitar NFF ranar Laraba ta ce kwamitin zartarwata ne ya amince da naɗa Peseiro ne bayan raba gari da Mr Gernot Rohr

Labarai Makamanta