Wasa Da Sallah Na Haifar Da Masifu – Imam Jabir Isah

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

An Bukaci Al’umma Musulmi su Rika Zuwa masallacin Juma’a akan Lokaci Domin Rabauta da Babbar Garabasar Ladar da ake Samu ga duk Mutumin da ya Halarci Masallacin Juma’a da Wuri

Wannan Kira ya fitone daga Bakin Imam Jabiru Isah Babban Limamin Masallacin Juma’a na Unguwar Nassarawa dake Karamar Hukumar Chukun a Jihar Kaduna a lokacin da yake Gabatar da Hadubar Sallar Juma’a

Imam Jabiru Isa ya kara da cewa ba daidai bane Mutum ya zauna a gida, ba tare da wata lalura mai karfi ba har sai yaji Liman ya fara Huduba sannan ya fito a guje, inda ya bayyana hakan a matsayin Rashin Girmama Addinin Allah SWT.

Daya juya kan batun kiyaye Sallah da Yinta akan Lokaci Kuwa, Imam Jabiru Isa Yace ba karamin laifi bane musulmi ya rika yin wasa da Sallah, kuma Hakan Yana Janyo Bala’o’i a tsakanin Al’aslalumma, Inda ya yi kira ga jama a da cewa duk wanda aka lura yana wasa da sallah ko kuma yabar Sallar Matakin Farko ga Alumma su fara masa wa azi, idan yaki dainawa kamata yayi a kyamaceshi wajen Muamala da makamantansu

Imam Jabiru Isa yaci gaba da cewa hatta Aure bai kamata aba mutumin dake wasa da sallah ba, sai dai ya nuna takaicinsa kan yadda yanzun irinsune ma akafi basu Aure kai tsaye, sai kaga Malamin Islamiyya ya gagara samun Mata amma anba wancen mai wasa da sallar.

Daga karshe yayi fatan masu yin wasa da Sallah su tuba su daina Domin samun Babban Rabo a Gobe Kiyama

Sannan Ya Nemi Jama a Da a kara dagewa da Addu’a a koda yaushe Domin Itace Maganin Masifun da Muke Ciki a Haliln Yanzun.

Labarai Makamanta