Wahala Da Tsadar Rayuwa Sun Karu A Tarayyar Najeriya – Hukumar Kididdiga

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar Kididdiga ta ƙasa ta ce an samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki a watan Janairun 2023.

Hukumar ta ce ta sanar a ranar Laraba cewa hauhawar farashin kayayyakin ya haura zuwa kashi 21.82 cikin ɗari idan aka kwatanta da kashi 21.34 cikin dari a watan Disamba.

Rahoton ya yi nuni da cewa hauhawar farashin kaya a shekara ya kai kashi 6.22 bisa ɗari idan aka kwatanta da na watan Janairun 2022, wanda ya kai kashi 15.60.

Rahoton ya ce kayayyakin da farashinsu ya tashi sun haɗa da burodi wanda ya kai kashi 21.67 da dankali da dawa, da doya da kuma na kayan lambu.

Bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa farashin kayayyakni a cikin Janairu 2023 yana kashi 1.87 a kowane wata.

Haka na zuwa ne yayin da ‘yan ƙasar ke ci gaba da fuskantar matsalar ƙarancin sabbin takardun kuɗi sakamakon sake fasalin kuɗi da gwamnati ta yi.

Matsalar ta jefa ‘yan ƙasar da dama cikin wahalhalu, inda suke fuskantar kalubale wajen biyan bukatun yau da kullum.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta yi gargaɗin cewa wannan manufar na iya jefa tattalin arzikin ƙasar cikin wani mawuyacin hali.

Labarai Makamanta

Leave a Reply