Wadata Sojoji Da Makamai Ne Zai Magance Matsalar Tsaro – Babangida

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, yayi kira ga gwamnatin yarayya ta horas da jami’an soji tare da wadata su da makamai na zamani domin magance matsalar tsaro dake addabar kasar nan.

Babangida wanda ya nuna matuƙar damuwarsa kan halin da ake ciki na rashin tsaro yace ya kasance yana taimakawa da bayar da shawarwari ga gwamnati ba tare da kowa ya sani ba, domin a gudu tare a kuma tsira tare.

Tsohon Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da manema labarai a gidanshi dake Mina babban birnin Jihar Neja ranar Sallah, Yace ya zama wajibi ga kowane ɗan ƙasa ya nuna goyon bayansa ga gwamnati da jami’an tsaro domin su kawo ƙarshen matsalar tsaron da ake fama da shi a wannan ƙasa tamu Najeriya.

Yayin da aka tambayesa ko yana ganin waɗanda ke kan madafun iko suna wasa da lamarin kawo ƙarshen matsalar tsaro, Babangida yace: “Akwai abubuwa da yawa da ya kamata su gyara, idan suka amince suka sake zama da tunani akan lamarin, ina da yaƙinin zasu samu nasara cikin sauki.”

Yayin da yake jawabi akan abinda ya kamata masu mulkin ƙasar nan a yanzun suyi, yace: “Ku samar wa soji duk abinda suke buƙata, sannan ku tunasar dasu cewa wannan ƙasar su ce, kuma basu da wata ƙasa data fi ta.”

“Sojin Najeriya na buƙatar makamai irin na zamani kuma suna buƙatar a horas da su. Ba wai kawai a siyo makamai a miƙa musu ba, ya zama wajibi a horas dasu yadda zasu yi amfani da makaman.”

A ƙoƙarin da yake na taimakawa da shawarwari ga gwamnati domin ganin an kawo ƙarshen wannan matsala, wadda a yanzun take nema ta mamaye mahaifarsa, jihar Niger, Babangida ya cigaba da cewa: “Muna bada shawara dai-dai gwargwado, bamu yayata duk abinda muka faɗawa gwamnati.

Ya zama wajibi mu haɗa kan mu, mu taimakawa waɗanda ke kan madafun iko, dukkan mu muna aiki ne don cimma kudiri ɗaya.” “Matsalar tsaro da rashin zaman lafiya, kowace gwamnati tana da nata ƙalubalen, ina tuna yadda muka yi yaƙi na tsawon shekara uku, a lokacin mutane sun taimaka wa gwamnati, gwamnati ta yi iya bakin ƙoƙarinta.”

“Ba wai a Najeriya ne kaɗai ake samun irin wannan matsalar ba, kasashe da yawa sun shiga irin wannan, wasu saida suka ɗauki shekara 10 kafin su samu nasarar magance komai, ina da yaƙinin cewa watarana Najeriya zata fita daga cikin wannan ƙangin.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply