Uwargidan Shugaban Kasa Ta Tura Ma’aikatanta Hutun Dole


Rahoton dake shigo mana daga Birnin tarayya Abuja na bayyana cewar uwargidan shugaban ƙasa Aisha Muhammadu Buhari, ta umarci ma’aikatan ofishinta su fara hutun sai baba ta gani, a wani ɓangare na tunkarowar ƙarshen shekara da kuma bikin kirsimeti.

Cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafinta na Instagram, an bayyana cewa za a rufe ofishin ɗungurngum, har abun da hali ya yi.

”Za a iya riƙa gudanar da muhimman ayyuka ta Internet kamar yadda aka yi a baya’, don haka daga yanzu kowa ya tafi hutu sai an ji daga garemu’ kamar yadda aka sanar da ma’aikatan cikin wannan sanarwa da ke ƙasa.

Labarai Makamanta