Uwargidan Ganduje Za Ta Tsaya Takarar Sanata

Mai ɗakin gwamnan jihar Kano Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta fara shirye-shiryen neman kujerar ɗan majalisar dattawa a shiyyar Jigawa ta Yamma maso Gabas a zaɓen shekarar 2023 da ke tafe.

Wata majiya mai ƙarfi da ta ke kusa da Dakta Hafsat Ganduje wacce ƴar asalin ƙaramar hukumar Malam Madori ce da ke jihar ta Jigawa, da ta buƙaci mu sakaye sunanta ta bayyanawa Labarai24 cewa tabbas akwai shirin yin takarar na Hafsat Ganduje ɗin.

Majiyar ta ƙara da cewa tuni shirye-shirye sun yi nisa domin har ta fara tuntuɓar masu ruwa da tsaki tare da kungiyoyin matasa da ke mazaɓar ta Jigawa maso gabashin jihar.

“Maganar gaskiya akwai maganar takarar da Gwaggo ta ke shirin yi a jihar Jigawa, amma kawo yanzu ba ta fito ta sanar ba”

“Domin ko a lokacin da ake sabunta katin rijistar jam’iyyar APC, to ba na Kano ta yi ba, kuma ba ta bayyana cewa ta tafi Jigawa ta yi ba. Har gida aka zo aka yi mata daga jihar ta Jigawa”

Lokacin da aka sabuntawa Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje katin jam’iyyar APC

Aikin samar da rijiyoyin burtsatse a mazabun karamar hukumar Malam Madori da Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta yi. Haka kuma wakilin Labarai24 ya je har ƙaramar hukumar Malam Madori inda nan ne mahaifar Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje din inda ya samu zarafin tattaunawa da wasu daga cikin al’ummar wannan karamar hukuma.

“Littattafai masu ɗauke da hoton Dakta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje da aka raba a wasu makarantun jihar Jigawa”

Alhaji Ɗankano Mai Yadi ɗaya ne daga cikin dattawan ƙaramar hukumar Malam Madori ya bayyana cewa duk abin da Hafsat Gandujen za ta nema suna goyon bayanta ɗari bisa ɗari.

“Duk abin da mai girma Gwaggo za ta nema ko ma meye muna goyon bayanta ɗari bisa ɗari, saboda irin yadda ta ke taimakon al’ummar mahaifarsa”

Shi ma wani matashi mai suna Hashim Malam Madori cewa ya yi a shirye su ke wajen baiwa Gwaggon gudummawa a dukkanin wata kujera da za ta nema.

“Game da ra’ayina akan tsayawar Gwaggo takarar ina goyon baya ɗari bisa ɗari, domin matar nan ta nuna mana halacci kuma ta nuna mana ita cikakkiyar ƴar Malam Madori ce mai kishin Malam Madori, saboda haka ina ra’ayi kuma na goyi baya”

Haka kuma Dakta Hafsat Ganduje ta samar da rijiyoyin burtsatse a mazabun da ke ƙaramar hukumar Malam Madori tare kuma da raba littafai ga makarantun yankin, wanda al’ummar wannan yankin ke kallon hakan a matsayin sharar fage ne na yin takarar.

Hafsat Abdullahi Umar Ganduje wacce Malama ce a jami’ar Bayero kuma tana da tasiri a cikin harkokin gwamnatin Kano za ta fafata da Barista Ibrahim Hassan Hadejia, wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin gwannan jihar ta Jigawa kuma shi ne ke wakiltar mazaɓar Jigawa ta Yamma maso Gabas a zauren majalisar dattawan ƙasar nan.

Haka kuma ƙananan hukumomi guda takwas ne ke karkashin wannan mazaɓa. Ƙananan hukumomin da su ka haɗa da Auyo da Birniwa da Guri da Hadejia da kuma Kafin Hausa.

Sauran ƙananan hukumomin sune Kaugama da Kirika Samma da sauransu.

–Labarai24

Labarai Makamanta