Ummi Zeezee Ta Mutu Ta Dawo


Fitacciyar jarumar finafinan Hausa, Ummi Ibrahim (Zee-Zee), ta dawo gida a jiya, a ranar da ake sa ran za a kawo gawar ta kamar yadda wani ya yi iƙirari.

Wata ƙwaƙƙwarar majiya mai kusanci da jarumar ce ta faɗa wa mujallar Fim hakan a daren jiya.

Majiyar ta ce Zee-Zee ta dawo gida ne a jiya Litinin, “kuma lafiyar ta ƙalau”.

Sai dai kuma majiyar ba ta yi ƙarin bayani ba, illa dai ta ce mu jira zuwa yau.

A yau ɗin kuma sai majiyar ta ce, “A dai faɗa wa duniya cewa Ummi ta dawo, kuma lafiyar ta ƙalau.

“Kuma in-sha Allahu zuwa anjima za mu sanar da ku abin da ya faru. Sai dai babu shakka yanzu haka ta na gida, kuma lafiyar ta ƙalau.”

Idan kun tuna, a shekaranjiya ne labari ya yaɗu cewa wai jarumar ta rasu a gidan wata ƙawar ta a Kaduna.

Amma wata hukumar tsaro da mujallar Fim ta tuntuɓa a Kaduna kan lamarin ta gano cewa wayar Zee-Zee ta na cikin yankin Sabo Garin a birnin Kano.

Haka kuma binciken da rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna ta yi ya gano babu wata gawa da aka samu a jihar da sunan ta Zee-Zee ce.

Abin da ya ɗaure wa mutane kai shi ne yadda aka tura saƙon ‘mutuwar’ ta hanyar wayar Zee-Zee ɗin da sunan wata ƙawar ta wai Khairat.

Amma Hasina Ɗan-Chaina, ƙanwar Zee-Zee da ke aure a Jos, ta bayyana cewa ita dai a iya sanin ta babu wata ƙawar Zee-Zee mai wannan sunan.

Tun a ranar da abin ya faru dai Hasina ta bayyana tababa game da mutuwar da aka ce yayar ta ta yi.

Yanzu kuma da Zee-Zee ta dawo gida, mutane za su ci gaba da tambayar me ya faru har aka tura saƙo ta hanyar wayar ta cewa ta rasu.

Wasu tambayoyin su ne: shin wanene ya tura saƙon? Wace manufar ake so a cimmawa? Ina Zee-Zee ta je ta kwana a daren Lahadi? Ya aka yi ta dawo gida? 

Wasu tambayoyin su ne: ina mutumin nan da ya riƙa kiran su Hasina Ɗan-Chaina ya na cewa shi ɗan sanda ne, wai gawar Zee-Zee na hannun sa, kuma wai za su kai gawar gidan su jarumar a jiya? Me ya sa ba su kai gawar ba?

Ana sa ran kila nan da wani lokaci Zee-Zee da kan ta za ta fito ta amsa wa jama’a waɗannan tambayoyin.

Duk wannan badaƙalar dai ta faro ne daga ranar 3 ga Afrilu, 2021 lokacin da Zee-Zee ta tura saƙo a Instagram cewa ta yanke shawarar za ta kashe kan ta.

Washegari kuma ta fito ta ce wani Ibo ne ya damfare ta kuɗi har naira miliyan 450, wanda hakan ya haifar mata da ciwon damuwa (depression) har ta ji gara ma ta mutu ta huta.

Mutane da dama sun soki jarumar kan wannan badaƙalar, su na cewa ita ce ta kitsa ta, kuma ta na yi ne domin ta ɗau hankalin jama’a, ba wai don gaskiya ba ce.

Wasu kuma sun ce ciwon damuwa da gaske ne, don haka sun yi addu’ar Allah ya ba ta lafiya.

Labarai Makamanta