Turnuku: Badakalar Kwangila Ta Raba Kan Manyan Kusoshin Gwamnati


Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wani rikici mai kama da ‘turnuƙu faɗan ibilisai’, wai yaro bai gani ba balle ya raba, ya ɓarke a Fadar Shugaban Ƙasa, tsakanin Ministan Sufuri Rotimi Amaechi da Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Tarayya, Ibrahim Gambari.

Ministan Harkokin Sufuri Ameachi ya zargi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Gambari da yi masa katsalandan a tsarin bayar da kwangila a ma’aikatar sa.

Wannan dai shi ne rikici na baya-bayan nan da ya fito fili tsakanin manyan jami’an gwamnatin Buhari.

Ameachi dai a cikin wani raddi, ya zargi Gambari da yi masa katsalandan a buga tandar zaɓen kamfanoni biyu daga cikin kamfanonin da suka nemi a ba su kwangilar Aikin Sa-ido Kan Manyan Jiragen Ruwa Masu Dakon Kaya (ICTN).

Wannan gagarimin aikin kwangila dai a Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen Ruwa za a yi shi, wadda ke ƙarƙashin kulawar Minista Amaechi.

Binciken mu ya gano cewa Shugaba Buhari da Minista Amaechi sun bayar da kwangilar lamari na tsaro a jiragen da tashoshin ga kamfanoni biyu wato MedTech Scientific Limited da Rozi International Limited.

Binciken dai ya nuna Buhari da Amaechi sun karya doka, ƙa’ida da cancantar bayar da kwangilar ga kamfanonin da ba su cancanta ba.

Kenan an karya ƙa’idar da ke shimfiɗe a cikin dokokin Hukumar Tantance Kwangiloli (BPE).

Yayin da Premium Times ta gano cewa MedTech Scientific Limited kamfanin sayar da magunguna ne, shi kuma Rozi International Limited kamfanin hada-hada da duoalncin manyan gidaje ne.

Amaechi ya samu nasarar kauce wa ƙa’idar da BPE gindaya, har ya samu Buhari ya sa masa hannun amincewa kan kwangilar.

Labarai Makamanta