Tuntuben Harshe Na Yi A Batun Daukar Matasa Miliyan 50 Soja – Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Alhaji Bola Ahmad Tinubu, ya yi gyaran fuska akan kalamin da yayi na a ɗauki sojoji matasa Miliyan 50 aiki, inda ya ce ba yana nufin gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 50 miliyan aikin soja ba, 50,000 yaso faɗa bakinsa ya kuɓuce.

Bola Tinubu yayi gyara kalamansa ne a ranar Talata inda yace suɓutar baki ne yasa ya faɗi haka amma shi mutum 50,000 ya so cewa, a domin haka ya bukaci jama’a suyi mishi uzuri.

An ga Tinubu na faɗa a wani bidiyo da ya mamaye kafafen sada zumunta cewa, gwamnatin tarayya ta ɗauki matasa 50 miliyan aikin soja don ta ƙarfafa yaƙin da take da ta’addanci wanda ya dabai-bayeta.

Jagoran jami’iyya mai mulki ya faɗi haka ne a wajen taron bikin cikarsa shekaru 69 a duniya ranar Litinin, 29 ga watan Maris. “Ku ɗau matasa miliyan 50 aikin soja” Tinubu ya faɗa a wajen taron yana mai ƙarawa da cewa duk abinda zasu ci muna da su a ƙasar nan.

Mai taimaka wa Tinubu ta fannin yaɗa labarai, Tunde Rahman, ya shaida cewa, yana nufin gwamnati ta ɗauki matasa 50,000 ne ba miliyan 50 ba kamar yadda ya faɗa a baya.

Sai-dai tun daga lokacin da ya yi wancan magana, ta jawo hankulan mutane da yawa a kafafen sada zumunta musamman tuwita.

Labarai Makamanta