Tuni Fim Din Labarina Ya Kare Sai Kame-Kame – Aliyu Gora ll

Shirin fin din labarina mai dogon zango na kamfanin saira movies ya ja hankalin jama’a da dama tun lokacin da aka fara haska shi a gidan talabijin na arewa 24 tun daga zango na farko har zuwa na hudu da ake ciki a yanzun,

Saidai Kuma tsohon editan jaridar fim dinnan wanda yanzu shine babban editan hausa na sha sashen labaru da Alamuran yau da kullum na tashar Talabijin ta liberty ya bayyana cewa Shifa a fahimtarsa tuni fimdin ya kare ko kuma basirar marubucin ta kare domin yanzun kame kame kawai akeyi, yayi wannan bayanine a shafinsa na sada Zumunta na facebook a ranar lahadin da ta gabata, wannan Rubutu nasa ya sa wasu daga cikin wadanda suka tofa albakacin bakin a bangaren yin comment wato sharhi da dama daga cikinsu sun goyi bayan Aliyu Gora II, Ya yin da wasu ke ganin a’a adai jira tukuna aga yadda zata kaya,

ko a kwanakin baya kafar yada labarai ta muryar Amurka sunyi hira da Malam Aminu saira akan batun, inda ya nuna cewa bazai tona sirrin da ke cikin fim din ba adai ci gaba da bibiyarsu duk amsoshin tambayoyin na cikin fim din

Zamu ci gaba da bibiya domin gano ahin da gaske ya kamata ace fim din ya kare kokuwa da saura?

Labarai Makamanta