Tun Kafin Hawan Buhari Mulki Jama’ar Daura Ke Neman Jihar Bayajidda – Salanken Daura

An bayyana cewar jama’ar masarautar Daura dake jihar Katsina sun dauki tsawon lokaci suna neman ayi musu Jigar Bayajidda daga Jihar Katsina tun kafin hawan Buhari karagar mulki.

Mai girma Salanken Daura babban ɗan Majalisar Sarkin Daura Alhaji Salisu Yusuf ne ya bayyana hakan lokacin da yake bayyana farin cikinsu akan tantance sunan Jihar Bayajidda da Majalisar ƙasa ta yi na wadanda suka cancanta ayi musu jiha a Nijeriya, a wata ganawa da manema labarai a Kaduna.

Salanken Daura ya kara da cewar sabuwar Jihar Bayajidda ta ƙunshi ƙananan hukumomi 11 na mazaɓar Daura da ƙarin wasu kananan hukumomi uku daga Jihar Jigawa wadanda suka haɗa da Kazaure da Ɓaɓura.

Basaraken ya godewa dukkanin al’ummar yankin tun daga kan Sarakuna da ‘yan siyasa da sauran jama’a waɗanda suka bada gagarumar gudummawa da goyon baya wajen ganin buƙatar neman Jihar ya tabbata.

“Ga Allah muke neman Jihar Bayajidda bisa ga yakinin da muke dashi na cancanta, addu’ar abin da yake alheri Allah ya tabbatar mana Allahumma Amin”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply