Tu’ammali Da Kwayoyi Na Taka Rawa Wajen Tabarbarewar Tsaro – Marwa


Shugaban hukumar yaki da fatauci da ta’amulli da miyagun kwayoyi, NDLEA, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai murabus) a ranar Alhamis, ya koka gami da yin gargadi kan karuwar ta’amulli da miyagun kwayoyi a Nijeriya, da rawar da hakan ke takawa wajen gurbatar tsaro.

A cewarsa, masu garkuwa da mutane da sauran bata gari sun fara neman a biya su fansa da miyagun kwayoyi a maimakon kudi kafin su sako wadanda suka sace, wanda hakan babbar barazana ce ga harkar tsaro.

Sanarwar da kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya fitar ta ce Marwa ya nuna damuwarsa kan batun ne yayin kaddamar da “kwamitin ayyuka na musamman” na hukumar kan yaki da ta’amulli da miyagun kwayoyi da safarar su.

Ya kuma yi kira ga yan Nijeriya su bada gudunmawarsu kan yakin da ta’amulli da miyagun kwayoyi a kasar. Marwa ya ce amfani da miyagun kwayoyi ya zama annoba ya kai kimanin miliyan 15 don haka ba abin mamaki bane ganin yadda aka samu karuwar miyagun laifuka kamar garkuwa da mutane, ta’addanci, kisan kai, fashi da saransu.

“Duk laifukan na da alaƙa da shan miyagun kwayoyi. Yanzu miyagu na neman a biya su fansa da miyagun kwayoyi, idan ba mu magance wannan matalsar ba, bata gari za suyi ta karuwa a kasar.

“Gashi kuma abin baya nuna wa a fuska, amma dukkan mu mun san wani ko wanda ya san wani da ke shan miyagun kwayoyi don haka akwai bukatar mu hada kai a matsayin yan Nijeriya don yaki da matsalar.

Labarai Makamanta