Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina Ya Rasu

Allah Ya karbi ran tsohon Shugaban majalisar dokokin jihar Katsina Kabir Ahmad Kofa bayan fama da rashin lafiya.

Kabir Ahmad Kofa ya rasu ne a daren Asabar wayewar Lahadi a wani asibiti dake a cikin birnin Katsina.

Kabir Ahmad Kofa ne shugaban majalisar dokokin jihar Katsina daga shekarar 1999 zuwa 2007, daga nan ya zama dan majalisar wakilan Nijeriya a shekarar 2007 zuwa 2011 duk a jam’iyyar PDP.

Bayanai sun ce za a gabatar da jana’izarsa da misalin karfe goma na safiyar Lahadin nan a masallacin GRA Katsina.

Labarai Makamanta