Tsohon Shugaban Ƙasa Murtala Ya Cika Shekaru 45 Da Rasuwa

An kashe tsohon shugaban Najeriya Janar Murtala Ramat Muhammad ne a ranar 13 ga watan Fabrairun shekarar 1976 a Legas.

Janar Murtala Ramat Muhammed ya taka rawar gani a yakin basasar da aka yi a shekarar 1967 lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu ke neman balle yankin Biafra daga Najeriya.

A wannan lakacin janar Murtala ya jagoranci rundunar sojin da suka murƙushe sojojin Biafra tare da kawo karshen yaki basasar baki ɗaya kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekarar 1967.

Yana matsayin birgediya ne sojojin da suka yi juyin mulki na uku a Najeriya suka naɗa Murtala a matsayin shugaban kasa , inda a watan Janairun shekarar 1976 aka kara masa girma zuwa janar mai anini hudu, wato kololuwa kenan.

Yana cikin shugabannin da aka yi a Najeriya da da ke da ƙima ga ƴan ƙasar.


Duk ranar 13 ga watan Fabrairu Ƴan Najeriya na tuna wa da Janar Murtala wanda ya fara tunanin dawo da babban birnin Tarayya daga Legas zuwa Abuja.

Sannan ƴan Najeriya na yi wa Janar Murtala da aka yi wa kisan gilla addu’ar samun gafarar Ubangiji

Labarai Makamanta