Tsohon Mataimakin Shugaban Amurka Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Rahotanni daga kasar Amurka na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, Mr Walter Fredrick “Fritz” Mondale ya riga mu gidan gaskiya.

Mr Mondale wanda ya rike mukamin mataimakin shugaban kasa karkashin gwamnatin Shugaba Jimmy Carter ya rasu ne yana da shekaru 93 a cewar mai magana da yawun iyalinsa.

Marigayin ya taba neman takarar shugaban kasa a 1984 amma bai yi nasara ba. Majiyoyi sun ce ya rasu ne a gidansa da ke Minneapolis duk da cewa ba a sanar da abin da ya yi ajalinsa ba.

“Lokaci ne ya yi. Na kosa in tafi in hadu da Joan da Eleanor,” Mondale ya ce a cikin wata sanarwar da ya rubuta ga ma’aikatansa kuma aka fitar bayan rasuwarsa.

“Kafin in tafi, ina son in sanar da ku irin muhimmancin da kuke da shi a wuri na.” Joan tsohuwar matarsa ce da ta rasu a shekarar 2014 sannan Eleanor yarsa ce da ta rasu a shekarar 2011 tana da shekaru 51 a duniya.

Mondale ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa karkashin Jimmy Carter daga shekarar 1977 zuwa 1981.

Labarai Makamanta