Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Koma APC

Tsohon kakakin majalisar wakilai kuma dan takarar Gwamnan Ogun a jam’iyyar ADP na 2019, Dimeji Bankole ya koma jam’iyya mai mulki ta APC.

Bankole ya gana da shugaban jam’iyyar APC, Shugaban Kwamitin Kula da Shirye-shiryen na babban taron (CECPC), Gwamna Mai Mala Buni a Abuja tare da rakiyar Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru.

Ganawar, wacce ta gudana a gidan shugaban jam’iyyar APC da ke Abuja, ta dauki kusan tsawon awa guda ana yin ta.

Dukkanin kokarin da manema labarai suka yi don samun ko da daya ne daga cikin shugabannin suyi magana ya ci tura yayin da taron ya zama na sirri amma sun dauki hotuna.

Amma wata gajeriyar sanarwa daga Malam Mamman Mohammed, Darakta Janar na Harkokin Labarai ga Gwamna Buni, ta tabbatar da taron. Ya ce: “Shugabannin uku sun tattauna kan batutuwa da dama na siyasa da suka hada da shigar tsohon Shugaban majalisar da magoya bayansa zuwa cikin jam’iyyar ta APC.”A bayyane yake cewa damar APC a jihar Ogun na ci gaba da fadada.”

Dangane da ci gaban, Shugaban jam’iyyar ADP na kasa, Engr. Yabagi Sani, ya fada wa The Nation cewa jam’iyyarsu ba ta ji dadin matakin da Bankole ya dauka ba.

Na yi tunani duba da shekarunsa da gogewarsa, zai nuna kyakkyawan misali. Matakin da ya dauka ya fi bakanta rai amma ba mu karaya ba.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply