Tsoffin Shugabannin Tsaro Sun Ci Kuɗin Makamai

Mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron ƙasa Janar Babagana Monguno mai ritaya ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka ba tsaffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta’addan Boko Haram, amma tabbas tsoffin Shugabannin tsaro ne suka cinye ta.

Janar Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da gidan rediyon BBC Hausa ranar Juma’a, 12 ga Maris.

Monguno ya kara da cewa sabbin hafsoshin tsaron da Buhari ya nada kwanakin baya basu ga kudaden ba, hakazalika basu ga makaman da aka ce an saya da su ba.

”Babu wanda ya san abin da aka yi da wadannan kudaden, amma da yardar Allah shugaban kasa zai bincika domin a gano inda aka kai su ko kuma a ina kayan suka shiga,” in ji Monguno.

”Tun da dai ba a yi wani binciken kwarai ba, ba zan ce wani abu ba, amma dai kudi dai tabbas sun salwanta, kayan dai ba a gani ba, kuma sabbin shugabannin tsaro sun ce su fa ba su ga kayyakin tsaro da ake magana ba a kai.”

“Ƙila wasu suna kan hanya daga Amurka, daga Ingila ko daga wasu wurare, amma yanzu a kasa ban gani ba su ma ba su gai ba,” in ji shi.

Tsaffin hafososhin tsaron sune Janar Abayomi Olonisakin; Lt-Gen. Tukur Buratai, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas;Air Marshal Sadique Abubakar.

Labarai Makamanta