Tsohon Kakakin majalisar wakilai daga jihar Kano, Ghali Umar Na’abba ya bayyana cewa cire tsohon satkin Kano, Muhammad Sanusi II daga Sarauta da Gwamnatin jihar ta yi bai kamata ba.
Yace idan aka kalli yanayin cire sarkin, hakan na nuna misalin yanda masu mukaman shugabanci ke amfani da karfin siyasa ba ta hanyar data kamata ba.
Ghali ya bayyana hakane a hirar da yayi da Sunnews. Yace duka idan ka kalli yanda Majalisar jihar Kano cikin sauri ta amince da kudirin dokar da ya bayar da damar sauke Sarkin, abune da ba’a yi shi bisa tsari ba.
Yace daukar mataki irin wannan, wanda zai taba rayuwar mutane, musamman ta hanyar da bata kamata ba, cikin sauri ba tare da jin ta bakin jama’a ba na nuna irin mulkin da ake ciki da kuma kalar ‘yan Majalisun da ake dasu.
Yace hakan na nuni da abin takaicin cewa yawancin ‘yan Majalisar Jihohi sun zama na jeka na yika, ‘yan amshin shata ne kawai.
Yace babu wanda zai yadda cewa cire Sarki Sanusi da kyakkyawar Manufa aka yi ta kuma an cireshi daga mukaminne bayan da ya bayyana ra’ayinsa akan cin hanci da aikata ba daidai ba.
You must log in to post a comment.