Shugaban Muhammadu Buhari ya gwale ‘yan majalisar dattawan kasar inda ya ki yarda da kiran da suka yi masa ya sauke hafsoshin tsaro.
A wata sanarwa da fadar shgaban kasar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce nadawa da sauke hafsoshin tsaron yana hannun shugaban kasa don haka shi kadai ne zai yanke hukunci a kan makomarsu.
A yau Talata ne dai majalisar dattawa ta amince da kudurin da ya yi kira ga hafsoshin tsaro su sauka daga mukamansu ko kuma a cire su saboda tabarbarewar tsaron kasar.
Fadar shugaban kasa ta yi duba ga wannan kuduri, kuma tana jaddada cewa nadawa da cire hafsoshin tsaro alhakin shugaban kasa ne, kuma Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayinsa na Kwamadan rundunar sojin Nijeriya, zai yi abin da ya fi wa kasar nan alfanu.
You must log in to post a comment.