Tsawon Shekarun Mulkin ‘Yan Arewa Bai Amfani Arewa Ba – Ewuga

An bayyana yankin arewa a matsayin yankin da yake koma baya sosai ta bangarorin cigaba da walwala idan aka kwatanta yankin da sauran yankunan ƙasar duk da tsawon lokaci da ‘yan Arewa suka shafe suna mulkin ƙasar.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin tsohon mataimakin Gwamnan jihar Nasarawa kuma tsohon minista Sanata Solomon Ewuga a yayin tattaunawa da aka yi da shi a cikin wani shirin gidan talabijin na Liberty Abuja mai suna “State Of The Union”.

Ewuga ya kara da cewar a fili yake Arewa ta kasance cibiya ta talauci da baƙin Jahilci gami da taɓarɓarewar tsaro da yalwar marasa aikin yi duk da tulin shugabanni da yankin ya samar, inda ya bayyana su a matsayin taron tsintsiya ba shara domin rashin tsinanawa yankin komai.

Dangane da batun kalubale da yankin Arewa ke fama dashi kuwa Sanata Ewuga ya bayyana cewa akwai tufka da warwara tsakanin ɓangaren Shugaban ƙasa da hukumomin tsaro, duba da yadda shugaban kasar ya kwarmata cewar sace dalibai da aka yi a Jangeɓe shine na ƙarshe a tarihin ƙasar, amma abin takaici ba a je ko’ina ba sai gashi an koma gidan jiya.

“Tabbas wannan abin kunya ne ga wannan gwamnati wadda a zamanin yaƙin neman zaɓe ta ayyana babban abin da zata sanya a gaba shine magance matsalar tsaro, sai gashi an wayi gari a yau tsaro ya taɓarɓare a wannan gwamnatin fiye da gwamnatocin baya”.

Ewuga ya kuma nuna tsananin mamaki da takaicin shi akan yadda ‘yan Bindiga ke cin karensu ba babbaka musanman a sace ɗalibai da suke yi, inda yace a yanayin zamanin da ake ciki na wayewa da fasahar ilimin kimiyya, abin mamaki ne hakan na faruwa ba tare da an daƙile faruwar hakan ba.

Sanata Ewuga ya shawarci gwamnati da ta ƙara tsaurara tsaro akan iyakokin kasa, domin a ta wajen ne ake safarar makamai zuwa cikin Najeriya da ƙananan kuɗaɗe, inda ya shawarci Gwamnatin tarayya da yi wa tufka hanci.

Labarai Makamanta