Tsawaita Yajin Aikin ASUU Ya Haifar Da Rudani A Najeriya

‘Yan Najeriya da dama na ci gaba da zazzafar muhawara, musamman a shafukan sada zumunta, dangane da tirka-tirkar da a ke yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU, game da kin biyan malaman jami’o’i albashi saboda yajin aikin da suke gudanarwa.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta tsawaita yajin aikin bayan ganawar kwamitin zartarwa a hedikwatar Kungiyar da ke Jami’ar Abuja.

Kungiyar ASUU dai ta shiga yajin aiki ne a watan Fabrairu, saboda gaza biya mata tarin bukatunta daga bangaren gwamnatin tarayayyar kasar.

Hakan ne ya sa gwamnatin tarayya ta ki biyansu albashin watanni da suka shafe suna yajin aikin, saboda a cewarta malaman ba su yi aiki ba cikin wadannan watanni

To sai dai wannan batu na rashin biyan malaman albashi na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya, inda kungiyar ta sanya shi cikin sabbin bukatun da take so gwamnati ta amince da su kafin janye yajin aikin, suna masu cewa ba koyarwa ba ne kadai aikin malamin jami’a.

Labarai Makamanta