Tsautsayi: Dan Tauri Ya Farke Cikinsa Da Wuka A Kano

Wani ɗan tauri mai suna Nadabo Alhassan ya gamu da ɓacin rana, bayan da ya farke cikinsa da wuƙa a yayin bikin ƴan tauri.

An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a garin Gani, Ƙaramar Hukumar Sumaila a Jihar Kano a ranar Lahadi.

Tun da farko dai, a yayin bikin na ƴan tauri, Alhassan, ɗan shekara 40, ya zo ya yi kirari, ya yi kirari, sai kuwa ya riƙa daɓawa kan sa wuƙa a sassan jikinsa.

An rawaito cewa, a yayin da Alhassan ya rufe idonsa yana ta gabzawa kansa ƙarfe, ai kuwa sai abokansa na tauri su ka riƙa cewa “ya isa! ya isa!!”, amma ina, tsumin tauri ya tashi, sai kawai ga tumbin sa a waje.

Kafin ka ce kwabo, Alhassan, ɗan asalin garin Keta-bura, Ƙaramar Hukumar Ningi a Jihar Bauchi, ya faɗi cikin jini shame-shame.

Nan da nan a ka kira ƴan sanda, inda su ka bazamo , su ka kuma garzaya da shi asibiti.

Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni Kwamishinan Ƴan Sanda, Sama’ila Shu’aibu Dikko ya bada umarnin a garzaya da ɗan taurin asibiti.

To amma, duk wannan abun da a ke, Alhassan ya tsallake rijiya da baya, inda kakakin ƴan sanda ya tabbatar da cewa yanzu haka yana nan yana karɓar magani a asibitin Gani da ke Sumaila.

Labarai Makamanta