Tsaro: Za A Kone Dubban Babura A Abuja


Labarin dake shigo mana yanzu haka daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Rundunar ƴan sanda reshen Abuja da kuma hukumar kula da lafiyar ababen hawa VIO da wasu hukumomi sun haɗa hannu domin ƙona babura 1,500.

Sun bayyana cewa za a ƙona baburan ne domin jama’a na amfani da su wajen aikata laifuka kuma tuni an haramta amfani da su a cikin ƙwaryar Abuja.

Hukumomin sun ce duk da haramcin amma ana samun masu kunnen ƙashi suna karya dokoki wanda hakan ya sa za su ƙona baburan domin koya wa waɗanda suka karya doka darasi.

Labarai Makamanta