Rundunar dakarun Tafkin Chadi sun yi wa mayakan Boko Haram dirar mikiya inda suka hallaka da dama daga cikin su ta bangaren Nigeria, yayin da wasu ‘yan ta’addan kuma aka yi masu kofar rago daga Marwan a kasar Kamaru.
Kwamandan runduna ta daya ta dakarun kasasahen yankin Tafkin Chadi, Brigadier
General Bouba Dobekreo ya yi wa Muryar Amurka bayani dangane da hare-haren da suka kai a kasashen Nigeria da Kamaru, al’amarin da yayi sanadiyyar rugurguza baki dayan sansanonin mayakan Boko Haram na wannan shiyya.
Brigadier General Bouba Dobekreo ya kara da cewa mayakan sun yi kokarin arcewa yayin da suka yi ta tsallakawa kan iyakar Nigeria, sannan sojojin sun yi nasarar kwato wasu daga cikin kayayyakin yakin ‘yan ta’addan.
Allah Sarki Kasarmu Nijeriya, wata miyar sai a makwabta
Yaa Allah Ka ceci Nigeria daga makircin maciya amana Amin
You must log in to post a comment.