Hukumar Sojin Najeriya ta gargadi gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, kan yin kalamai marasa tushe da inganci kan jami’anta dake filin daga.
Wannan na cikin shawarwarin da kwamitin binciken da baiwa hakkin binciko gaskiyar maganar cewa Sojoji sun ajiye makamai suna noma da kiwon kifi a Baga.
Jagoran kwamitin Manjo Janar Felix Omogui, wanda shine mataimakin kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, ya yi hira da ‘yan jarida ranar Juma’a a Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.
Ya bayyana cewa wasu jami’an tsaro da ba Soja bane suka fara yayata jita-jitan kuma suka fadawa gwamnan. Janar Felix ya bayyana cewa lokacin da suka je garin Baga gane ma idanuwansu, babu alamun wani alaman noma ko kiwon kifi da ake zargin Sojin na yi.
“Haramcin yin noma da kiwon kifi a filin daga na cikin ka’idojin aikin Soja.” Yace Hukumar Soji ta kammala bincike kan harin da aka kaiwa Zulum.
Ya kara da cewa kwamitin binciken ya samu garin Baga cike da bama-baman da aka birne cikin kasa yadda ba za’a iya noma ba. “Wasu jami’an tsaro yan iya yi masu neman suna maimakon hada kai da ‘yan uwansu suke yada karerayi.”
“Gwamnan Borno kuma ya amince da wadannan zarge-zargen da aka yiwa Sojojin 19 a Baga bisa kalaman da yayi kwanan nan,” “Kalaman manyan mutane irin wannan zai iya ragewa Sojojin karfin gwiwa kuma zai iya munana tasiri kan yakin da ake yi da kuma cire yardar da mutane suke yiwa Sojoji.” Inji Janar Felix
You must log in to post a comment.