Tsaro: Najeriya Ta Tura Sojoji Kasar Mali

Labarin dake shigo mana daga Hedkwatar tsaro ta ƙasa na bayyana cewar an tura dakarun Sojojin Najeriya 62 dake cibiyar samar da zaman lafiya don tunawa da Martin Luther Agwai (MLAILPKC) kasar Mali don aikin samar da zaman lafiya.

An tura jami’an ne bayan makwanni uku ana musu horo bisa ka’idojin majalisar dinkin duniya, Kwamanda cibiyar (MLAILPKC), Manjo Janar Auwal Fagge ya bayyana.

Manjo Janar Fagge ya bayyana hakan ne a taron yaye Sojojin bayan horo a Jaji, jihar Kaduna. Yace: “Sashe farko na horon ya hada da kwarewa wajen rike makamai, da salon aikin soja.

Sashe na biyu na horon ya koyawa Sojojin yadda ake samar da zaman lafiya bisa sharrudan majalisar dinkin duniya.” “Hakazalika ya hada da darrusan yadda ake kare farar hula, yadda ake kare mata daga fyade da yara.”

Labarai Makamanta