Tsaro Na Samuwa Yanzu A Katsina – Masari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya yi zama da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa kan batun rashin tsaro.

Rt. Hon. Aminu Bello Masari ya jagoranci tawagar wasu manyan Katsina da suka zanta da Buhari dangane da halin rashin tsaro da Jihar ke ciki.

Rahoton yace tawagar ta hada da Sanata Abba Ali, Sanata Mamman A. Danmusa, Alhaji Aliyu Mohammed, Nalado Y, Sarkin Sudan da Alhaji Ahmed Yusuf.

A jawabin da ya gabatar Masari ya bayyana cewar “Abin da ya fi muhimmanci ga jihohi a yaki da ‘yan bindiga, musamman jihohin Arewa maso yamma shi ne mu hada-kai, mu toshe duk wata kafa.”

“Amma idan wata jiha ta na da tsarin da ya ci karo da na wata, shakka-babu, su (‘yan bindigan) za su bar wannan jiha, su koma wata jihar.”

Gwamna Masari ya bayyana cewa an yi dace, jihar Katsina ta na hada-kai da jihohi irinsu Neja da Nasarawa domin ganin an iya shawo kan matsalar tsaro a yankin.

Gwamnan ya yi magana a game da kashe kwamishinansa da aka yi har gida, yace kisan bai da alaka da ‘yan bindiga, yace wasu ne kurum su ka nemi ganin bayansa.

Sannan gwamnan yace abubuwa sun fara lafawa a jihar Katsina, yace ana ganin cigaba. A cewarsa, ba za a ce komai ya dawo daidai ba, amma da sauki yanzu.

Labarai Makamanta