Tsaro: Matawalle Ya Garzaya Neman Maganin ‘Yan Bindiga A Nijar

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamna Bello Matawalle a ranar Litinin, ya gana da shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, a wani bangare na kokarin kawo karshen duk wani nau’in ‘yan bindiga a Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Sakataren yada labarai na gwamnan, Jamilu Iliyasu Birnin Magaji, ya ce shugabannin biyu sun gana ne a fadar shugaban kasar dake birnin Yamai.

Gwamna Bello Matawalle ya samu rakiyar Sanata Sahabi Yau Kaura mai wakiltar mazabar Zamfara ta Arewa da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum a majalisar wakilai ta tarayya, Injiniya Suleiman Abubakar Mahmoud Gummi.

Hakazalika da babban sakataren gwamnatin jihar Lawal Umar Maradun da dai sauran manyan kusoshin gidan gwamnatin jihar.

Taron dai an yi shi ne domin tattauna batutuwan da suka shafi tabarbarewar tsaro musamman a yankin Arewa maso yammacin Najeriya da jamhuriyar Nijar tare da kudurta aniyar binciko wasu fannonin tallafi da hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Nijar da jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya yi wa shugaba Bazoum bayanin irin matakan da gwamnatinsa ke dauka na kawo karshen duk wani nau’i na miyagun laifuka a yankin. Gwamnan ya ce baya ga shirin zaman lafiya da sulhun da ya kaddamar, gwamnatinsa ta baiwa jami’an tsaro bayanan sirri kan yadda za a iya gano masu ba da bayanai ga ‘yan bindiga da abokan huldar su.

Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta bai wa gwamnatin Jamhuriyar Nijar tallafin sabbin motoci guda biyar don samar da aikin sintiri na musamman a Maradi da sauran sassan Jamhuriyar Nijar da ke kan iyaka da jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Gwamnan ya ce za a mika motocin ga Gwamnan Jihar Maradi a wani bikin da za a yi daga baya tare da amincewar Shugaba Mohamed Bazoum.” Ya bukaci a yi taro akai-akai kan harkokin tsaro da Ministan Tsaro na Nijar da Gwamnan Maradi da Gwamnan Jihar Zamfara da na Jihohin Katsina da Sokoto domin kawo karshen matsalolin tsaro da kasashen biyu ke fuskanta.

Da yake mayar da martani, Shugaba Bazoum ya gode wa Gwamna Bello Matawalle bisa wannan ziyarar da kuma duk wani kokari da ya yi na kawo karshen matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasashen biyu, musamman ma kan iyakar Maradi da Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shugaban kasa Mohamed Bazoum ya bukaci Matawalle da ya ci gaba da kokarin da ake yi na magance matsalar rashin tsaro a Zamfara ta hanyar samar da sabbin hanyoyin samar da zaman lafiya da aka riga aka samu a yankin. Ya kara da cewa gwamnatin Jamhuriyar Nijar a shirye take ta ba da goyon baya a yaki da rashin tsaro.

Labarai Makamanta