Tsaro: Mafarkin ‘Yan Najeriya Ya Kusa Tabbata – Magashi

Ministan tsaron Nijeriya Janar Bashir Salihi Magashi ya umarci dakarun sojojin Nijeriya da su ci gaba da matsawa ‘yan ta’addan Boko Haram dake addabar ‘yan Nijeriya a yankin Arewa maso gabas, da ‘yan ta’addan daji masu garkuwa da mutane a cikin yankin Arewa maso yamma da sauran yan ta’addan dake addabar kasar baki daya.

A cikin sakon da ministan ya saki, ya tabbatar wa da duniya cewa dakarun sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro na matukar kokari wajen dakile matsalar tsaron da ya addabi kasar.

Janar Magashi ya ci gaba da bayyana cewa insha Allahu mafarkin ‘yan Nijeriya zai tabbata na ganin dauwamammen zaman lafiya ya dawo cikin Nijeriya.

Muna rokon Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya a cikin kasar mu Nijeriya.

Labarai Makamanta