Tsaro: Gwamnati Ta Sako Tubabbun ‘Yan Boko Haram 600 Cikin Jama’a

A ranar Litinin, 13 ga watan Yuli, 2020, wasu tsofaffin ‘yan Boko Haram 600 su ka samu ‘yanci a Nijeriya bayan sun tuba daga mummunan aikin da su ke yi.

‘Yan Boko Haram din sun rabu da ta’addanci, sun tuba, sannan kuma sun shiga wani tsari da aka tanada domin sake rikidar da su da canza masu tunani.

Bayan kammala wannan shiri, tsofaffin ‘yan ta’addan sun rantse ba za su sake komawa cikin irin wannan danyen aiki na hallaka Bayin Allah da sunan addini ba.

Mai magana da yawun bakin dakarun sojojin kasa na Operation Safe Corridor, Manjo-Janar Bamidele Shafa ya ce tsofaffin ‘yan ta’addan sun yi rantsuwar biyayya ga gwamnati.

Bamidele Shafa ya shaidawa ‘yan jarida cewa wadannan mutane ba za su sake shiga Boko Haram ba. A baya ma an saki mayaka 1, 400 wadanda su ka fice daga Boko Haram.

Yanzu haka kuma akwai wasu ‘yan ta’adda 280 wadanda su ka nuna sha’awar fita daga kungiyar, su ma su na tsare a wannan cibiya ta rikida tunanin tsofaffin ‘yan ta’addan.

Jaridar Anadolou Agency ta ce an kama wadannan mayaka ne a yankin Borno, Adamawa da Yobe da ke Arewa maso gabas. Kawo yanzu ‘yan ta’addan Boko Haram sun kashe fiye da mutane 30, 000.

Bayan haka daga 2009 zuwa yanzu, sun fatattaki mutane miliyan uku daga gidajensu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply